Isa ga babban shafi
Sudan Ta Kudu

Machar ya samu mafaka a Congo

Shugaban ‘Yan Tawayen Sudan ta kudu kuma tsohon shugaban kasar Riek Machar ya samu mafaka a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo bayan ya fice daga kasar. Wani jami’insa ya ce Machar ya samu mafaka a Kinshasa kuma yana shirin tafiya Addis Ababa inda aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka sake nada shi mataimakin shugaban kasa.

Shugaban 'Yan tawayen Sudan ta kudu Riek Machar
Shugaban 'Yan tawayen Sudan ta kudu Riek Machar AFP Photo:UNMISS/Isaac Alebe Avoro
Talla

Tuni dai aka rantsar da Tabang Deng Gai daga bangaren 'Yan tawaye a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa.

Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyyar Congo ta tabbatar da cewa Machar yana cikin kasar tare da iyalin shi.

Rikici dai ya barke a Sudan ta kudu ne a 2013 tsakanin Dakarun gwamnatin Salva Kiir da kuma wadanda ke biyayya ga mataimakin shi Reik Machar.

Yarjejeniyar sulhu da bangarorin biyu suka amince ta gagara kawo karshen rikicin kasar da ta balle daga Sudan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.