Isa ga babban shafi
Zambia

Jam'iyyar adawa ta shigar da kara kotu

Dan takarar neman shugabancin kasar Zambia da ya sha kaye a zaben kasar Hakainde Hichlema ya shigar da kara kotun fasalta kundin tsarin mulki yana kalubalantar sahihancin sakamakon zaben da ya bawa Edgar Lungu damar sake darewa kujerar shugabancin kasar. 

Shugaban Zambia Edgar Lungu
Shugaban Zambia Edgar Lungu DR
Talla

Hichilema wanda ke jagorantar babbar jam’iyyar adawa a Zambia UNDP ya ce Shugaba Lungu bai samu adaddin kuri’u sama da kashi 50 da zasu bashi damar lashe zaben shugaban kasar ba, kamar yadda doka ta tanadar.

Hichilema wanda karo na biyar kenan yana neman shugabancin Zambia, na bukatar ganin an soke zaben da aka bayyana cewa Shugaba Edgar Lungu ya yi nasara da samun kashi 50.35% daga cikin kuri’un da aka kada yayinda shi kuma Hichilema ya samu kashi 47.63%.

A dokar kasar Zambia, kotun fasalta kundin tsara mulkin tana da kwanaki 14 na sauraren wannan kara, hakan yana nufin dole a dage batun rantsar da Lungu a matsayin sabon shugaban kasa da ake shirin yi a ranar Talata mai zuwa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.