Isa ga babban shafi
Malawi

An ki bayar da belin mutumin da ya sadu da mata 100 a Malawi

Mai gabatar da kara a Malawi ya ki bada belin Eric Aniva mutumin da ake tuhuma da laifin kwanciya da mata 100 da sunan ibadar tsarkake su. Karo na biyu ke nan ana yin watsi da bukatar shi.

Eric Aniva ya kwanta da Mata sama da 100 a Malawi
Eric Aniva ya kwanta da Mata sama da 100 a Malawi
Talla

Mai gabatar da kara Christopher Botoman ya ce ya yi watsi da bukatar belin ne saboda tsoron kada ya razana masu bayar da sheda a Kotu.

Mai gabatar da karan ya ce ba zai bayar da shi beli ba saboda girman laifin da ya aikata.

Aniva ya sadu da Mata 104 da sunan tsarkake su tare da zama mata na gari ga mazajensu.

Sannan bincike ya nuna mutumin mai shekaru 45 yana dauke da cutar Sida, kuma yana kokarin tserewa ne daga kasar zuwa Mozambique.

Ana zargin Aniva ne da saduwa da ‘Yan mata ‘yan kasa da shekaru 16 da kuma manyan mata. Kuma idan aka tabbatar da laifin da ake tuhumar shi na saduwa da kananan yara za a iya yanke ma shi hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.