Yara sun kamu da Cutar Polio a Najeriya
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace a karon farko bayan shekaru biyu an samu yara biyu da suka kamu da cutar polio a Najeriya, matakin da ya kawo koma baya dangane da shirin wanke kasar daga cikin masu fama da cutar.
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace yara biyun sun kamu da cutar Polio a Jihar Barno wanda hakan ya mayar da hannun agogo baya a kokarin da Najeriya keyi na wanke kanta daga kasashen dake fama da cutar.
Matshidiso Moeti, Daraktan hukumar dake kula da Afirka tace abin abin yi yanzu shine tabbatar da cewar an yiwa yaran dake Yankin rigakafi cikin gaggawa.
Doune Porter, jami’in sadarwa na hukumar UNICEF a Najeriya yace samun bullar cutar a Maiduguri ya biyo bayan wahalar da aka samu wajen yiwa yara rigakafin cutar a Jihar dake fama da tashin hankali.
Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha alwashin hada kai da hukumomin duniya dan tabbatar da kawo karshen cutar a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu