Isa ga babban shafi
Sudan

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 76 a Sudan

Akalla mutane 76 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa hade da ruwan sama da aka tafka a kasar Sudan, abinda ya shafi dubban gidajen jama’a.

Ambaliyar ruwa hade da ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 76 a Sudan
Ambaliyar ruwa hade da ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 76 a Sudan Reuters/路透社
Talla

Ministan cikin gidan kasar ne, Ismat Abdelrahman ya sanar da hakan a yau Alhamis, inda ya ce, ambaliyar ta shafi 13 daga cikin lardunan kasar 18.

Ma’ikatar ruwa da bunkasa noman rani ta kasar ta ce, kogin Nilo ya yi cikar da ba a taba gani irinta ba a cikin karni guda saboda ruwan saman da aka rika tafkawa kamar da bakin kwarya a sassan gabashin Afrika.

Kididdiga ta nuna cewa, kimanin gidaje dubu 3 da 206 ne suka rushe baki daya, yayin da gidaje dubu 3 da 48 suka lalace a lardin Kassala, daya daga cikin yankunan da ambaliyar ta fi shafa a Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.