Isa ga babban shafi
Nijar

China ta gina wa Nijar Asibitin zamani

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya kaddamar da sabuwar asibitin zamani da gwamnatin China ta gina wa kasar akan kudi Biliyan 45 na CFA. An gina asibitin ne a birnin Yamai mafi girma a kasar kuma tana dauke da gadajen majinyata 500.

Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou africtelegraph
Talla

Ministan lafiya Kalla Muntari ya ce sabuwar asibitin sauki ne ga al’ummar Nijar inda za su samu magani cikin rahusa tare da kaucewa zuwa kasashen ketare domin neman lafiya.

Asibitin kuma za ta kunshi kwararrun likitoci daga kasashen China da Cuba da kuma Turkiya.

Kiwon lafiya na cikin manyan kalubalen da Nijar ke fuskanta musamman matsalar Tamowa tsakanin Yara kanana.

China kuma na cin moriyar Nijar ta hanyar hako danyen mai da arzikin Uranium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.