Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba sauran cutar Polio a Najeriya

A yau Lahadi Najeriya ta yi bikin cika shekaru biyu ba tare samun cutar Shan-inna ba, a wani mataki da ake ganin nahiyar Afrika na dab da bankwana da cutar baki daya. Idan dai har babu wani da aka samu na dauke da cutar zuwa watan Yulin 2017, to hukumomin lafiya za su tabbatar da kawar da cutar baki daya a Najeriya.

Najeriya na murnar kawo karshen cutar Polio
Najeriya na murnar kawo karshen cutar Polio Getty Images/Ranplett
Talla

Cutar dai ta fi shafar yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar, wacce ke haifar da nakasar jiki ko mutuwa.

Ba a samu wanda ya kamu da cutar ba tun a watan Yulin 2014 da aka ruwaito wani yaro ya kamu da cutar a Jihar Kano.

A baya can dai, Najeriya ta kasance cikin kasashen da ke sahun gaba inda cutar ta fi kamari, amma yanzu kasashen Afghanistan da Pakistan ne akan gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.