Isa ga babban shafi
Afrika

Fari na tilasta wa yara aure da kwadago a Afrika

Kungiyoyin agaji sun ce matsalar sauyin yanayi ta El Nino ta haddasa fari a kasashen yankin kudancin Afrika, lamarin da a hannu daya ke tilasta wa yara kanana yin aure da kuma shiga ayyukan kwadago domin samun abin da za su ci.

Fari na tilasta wa iyaye aurar da 'ya'yansu mata da kuma shigar da su ayyukan kwadago
Fari na tilasta wa iyaye aurar da 'ya'yansu mata da kuma shigar da su ayyukan kwadago Jacky Ghossein-The Sydney Morning Herald/Fairfax Media via Getty
Talla

Matsalar sauyin yanayin ta haifar da karancin saukar ruwan sama a kasashen yankin na kudancin Afirka, lamarin ya haifar da cikas ga ayyukan noma a yankin baki daya.

Tuni iyaye suka fara aurar da ‘yayansu mata masu kananan shekaru, yayin da wasu ke shiga ayyukan kwadogo domin samun abinda za su ci da kuma iyalansu, kamar dai yadda kungiyoyin World Vision da Unicef da kuma Plan International suka sanar a wata sanarwa.

Matsalar dai ta fi shafar kasashen Lesotho da Malawi da Namibia da Swaziland da kuma Zimbabwe, inda kashi biyu cikin uku na al’ummomin wadannan kasashe sama da milyan 60 ke fama da karancin abinci.

Tuni kasar Afrika ta Kudu ta shelanta kafa dokar ta baci a takwas daga cikin lardunan kasar tara, yayin da Mozambique ta dauki irin wannan mataki a wasu yankuna da ke kudanci da tsakiyar kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.