Isa ga babban shafi
Najeriya

Twitter ya rufe shafin “Avengers”

Kamfanin Sadarwa na Twitter ya sanar da rufe shafin kungiyar tsagerun Niger Delta Avengers da ta ke amfani da shi wajen aika wa da sakwanninta ga jama’a.

Tsagerun Niger Delta da ke yi tattalin arzikin Najeriya barazana.
Tsagerun Niger Delta da ke yi tattalin arzikin Najeriya barazana. (Photo : Pius Utomi Ekpei/AFP)
Talla

Kungiyar Avengers ta dade tana amfani da Twitter wajen bayyana irin hare haren da ta ke kai wa da kuma sakwanninta ga al’ummar Najeriya.

Kamfanin ya ce ya dauki matakin ne saboda hana amfani da kafarsa wajen tayar da hankali da kuma barazana ga jama’a.

A ranar Lahadi tsagerun na Niger Delta sun yi ikirarin kai hare hare kan kadararoin gwamnati na hako mai tare da kai harin bom a kamfanin Chevron a Jihar Delta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.