Isa ga babban shafi
Najeriya

Senatocin PDP sun yanke goyon bayansu ga Buhari

‘Yan Majalisar dattawan Najeriya daga Jam’iyyar PDP sun sanar da kawo karshen goyan bayan da suke ba shugaban kasar Muhammadu Buhari sakamakon zarginsa da yin bita da kulli akan shugabanninsu a Majalisar.

Shugaban Majalisar Dattijai Dr Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu na ratsuwar kama aiki
Shugaban Majalisar Dattijai Dr Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu na ratsuwar kama aiki hopefornigeriaonline
Talla

Senatocin sun yanke goyon bayansu da Buhari saboda abin da suka kira yadda ya sa ‘ya’yan Jam’iyar su a gaba kan batun kudaden yakin neman zabe.

Bayan wani taro da Sanatocin suka yi, mataimakin bangaren marar rinjaye Emannuel Bwacha daga Jihar Taraba ya ce kokarin da ake na cire Shugaban Majalisar da Mataimakinsa ba za su amince da shi ba.

Senata Bwacha ya ce sun lura cewa bangaren Zartarwa na kokari ne domin sauya shugabannin Majalisar. A cewar shi suna goyon bayan yaki da Rashawa amma kuma gwamnatin Buhari na nuna son kai wajen farautar ‘Yan PDP.

Ana dai zargin Shugaban Majalisar Dattawa Saneta Dr Bukola Saraki da Mataimakinsa Ike Ekweremadu da laifin sauya dokokin Majalisa wanda ya ba su damar jagorantar Majalisar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.