Darajar Naira ta fadi
Darajar Naira ta fadi da kusan kashe 40 a yau Litinin bayan gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin da kasuwa za ta daidaita darajar kudin na Naira.
Wallafawa ranar:
A yau an sayar da dala akan Naira 280.50 a farashin gwamnati bayan soma aiwatar da shirin da Babban Bankin Najeriya ya ce zai farfado da darajar kudin kasar.
Amma a kasuwar canji ta bayan fage an sayar da dala ne akan Naira 350.
A can baya dai Babban Bankin Najeriya ya kayyade farashin Dala akan Naira 197 zuwa 199, matakin da ya jefa ‘Yan kasuwar mai cikin kasar cikin mawuyacin hali, saboda karancin kudin na kasashe waje a kasuwa.
Yanzu Babban Bankin na Najeriya ya bude kofa ga wasu kafofi da za a iya samun kudaden na waje sabanin hanya guda ta samun kudin daga bankin. Yanzu Kasuwa ce za ta daidaita farashin na Naira.
Masana dai na ganin za a dawo cinikin Naira akan Naira 250 a tsakanin bankuna karkashin kulawar Babban bankin Najeriya CBN.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu