Ranar 6 ga Yuli za a yanke wa Pistorius hukunci
A ranar 6 ga watan Yuli kotun Pretoria za ta zartar da hukunci akan dan tseren guragun Afrika ta kudu Oscar Pistorius, da ke fuskantar shari’a kan tuhumarsa da ake da kisan budurwar shi a ranar masoya.
Wallafawa ranar:
Kotun ta tsayar da ranar yanke hukuncin ne bayan kawo karshen sauraren karar na kwanaki uku a jiya Laraba
Tsohon zakaran gudun nakasasu Oscar Pistorius, ya cire kafafuwan shi na karfe a cikin harabar Kotu a jiya Laraba, domin nunawa kotun bukatar sallama a maimakon ci gaba da tsare shi.
A jiya dai mahaifin Reeva Steenkamp wadda Pistorius ya kashe, ya bukaci a yanke hukunci mai tsanani saboda aikata kisan budurwar shi.
Lauyan Pitorius ya yi bahasi a kotun domin nuna nasakar dan tseren guragun a yanayin da zai iya kashe budurwar shi
A 2013 ne ranar masoya ta Valentine Pistorius ya bindige Reeva a gidan shi a tsakiyar dare amma ya yi ikirarin bude wuta tunanin wani ne ya yi kokarin kutsowa cikin gidan a cikin dare.
Mai shigar da kara ya bukaci a yanke wa Pistorius hukuncin dauri na akalla shekaru 15 a gidan yari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu