Isa ga babban shafi
Najeriya-Opec

An nada Barkindo a matsayin sabon sakataren kungiyar Opec

A karshen taron da suka gudanar a birnin Vienna na kasar Austria, kasashe mambobi a kungiyar Opec sun zabi dan Najeriya Mohammed Barkindo a matsayin sabon sakataren kungiyar ta Opec.

Mohammed Barkindo, sabon sakataren kungiyar OPEC
Mohammed Barkindo, sabon sakataren kungiyar OPEC twitter
Talla

Barkindo ya maye gurbin Abdallah El Badri dan kasar Libya ne wanda ke rike da wannan matsayi tun shekara ta 2007, kuma Barkindo zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan agusta mai zuwa.

A taron na jiya alhamis kasashen duniya masu arzikin man fetur sun gaza cimma jituwa a tsakaninsu kan yadda za a kayyade adadin mai da ya kamata kowace kasa ta fitar zuwa kasuwar duniya a rana.

A karshen taron da suka gudanar a birnin na Vienna, kasashe mambobi a kungiyar ta Opec, sun ce an kasa cimma daidiato kan wannan batu, inda wasu ke cewa adadin gangar mai da ake fitarwa a rana ya wadatar, yayin da wasu ke cewa adadin ya yi yawa kuma akwai bukatar rage shi domin ko watakila farashin gangar mai zai tashi zuwa sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.