Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai ziyarci Neja Delta

Rahotanni daga fadar gwamnatin Najeriya sun ce shugaban kasar Muhammadu Buhari zai ziyarci Yankin Neja Delta ranar Alhamis mai zuwa domin kaddamar da shirin tsabtace Yankin Ogoni da aka gurbata.

Mutanen Ogoni a yankin Neja Delta mai arzikin fetir a Najeriya
Mutanen Ogoni a yankin Neja Delta mai arzikin fetir a Najeriya AFP PHOTO
Talla

Wannan ita ce ziyara ta farko da shugaban zai kai Yankin tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa shekara guda ta gabata.

Buhari ya ware makudan kudade domin ganin an gudanar da aikin tsabtace Yankin na Ogoni sakamakon gurbata shi da kamfanonin mai da kuma tsagerun da ke fasa bututun man suka yi.

Tun lokacin kamfen, Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki alkawalin tsabtace yankunan Neja Delta da aka gurbawa mutanen yankin muhallinsu da suke noma da kamun kifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.