Isa ga babban shafi
Najeriya

Ta’addancin Boko Haram ya durkusar da ilimi a arewa maso gabashin Najeriya

Yau shekaru biyu  kenan da mayakan Boko Haram suka kashe dalibai fiye 43 a makarantar gwamnatin tarayya dake Buni Yadi a jahar Yobe.

Wasu dalibai a wata Makaranta da ta ci wuta a garin Maiduguri
Wasu dalibai a wata Makaranta da ta ci wuta a garin Maiduguri AFP
Talla

Mayakan basu bar makarantar kwanan ba sai da suka kona illahirin ajujuwa da sauran kayyakin karatu kuma kawo wannan lokaci makarantar ta kasance kufai.

A wannan lokacin al’amarin ya tilastawa gwamnatin Yobe rufe makarantun jahar to sai dai bayan sake buda makarantun,  a halin yanzu iyayen yaran sun gagara aika 'ya 'yansu makaranta sakamakon bakin talauci da yankin ke fama da shi.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai, na baya baya a fannin ilimi a Nijeria sakamakon talauci tun kafin faruwar rikicin Boko Haram abinda yasa yanzu ake da yara sama da miliyan daya da basa zuwa makaranta, kamar yadda rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ke cewa, Majalisar ta kuma nuna takaicinta kan wannan al'amarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.