Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An gabatar da afuwa ga fursunoni dubu biyu a Zimbabwe

Kasar Zimbabwe ta gabatar da afuwa da fursunoni dubu biyu, da ake tsare da su a gidajen yari sakamakon cunkoson da ake fuskanta a gidajen kaso a kasar.

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Dukkanin fursunoni ‘yan kasa da shekaru 18, da kuma dukkanin mata da ake tsare dasu, sai wasu matan guda 2 da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai, an sake su a cewar jaridar The Herald.

Shugaban gidajen yarin kasar Priscilla Mthembo ya sanar da jaridar cewa, ba an saki fursunonin bane dan su je su yi abinda suka ga dama, kama ta yayi su yi amfani da wannan dama wajen gyaran hallayen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.