Isa ga babban shafi
Mali

An kai samame kan masu sayar da naman jakki

Hukumomi a kasar Mali sun kai samame tare da kama dimbin jama’a wadanda suka shahara ta fannin yanke jakki tare da sayar da naman a kasuwa, duk da cewa a karkashin dokokin kasar an hana sayar da naman jakkin.

Jakki a matsayin abin sufuri a Zinder na Jamhuriyar Nijar
Jakki a matsayin abin sufuri a Zinder na Jamhuriyar Nijar Sayouba Traoré/RFI
Talla

Tun da jimawa ne dai hukumomin kasar suka kafa dokar da ke hana cin naman jakki a kasar baki daya, lura da yadda jama’a ke yankawa tare da safarar namansa domin ci a cikin gida da kuma kasashe makota.

A garin Segou mai tazarar kilomita 240 a arewacin Bamako, ‘yan sanda sun kai samame a wata shahararriyar mayankar jakuna, wadda aka tabbatar da cewa daga nan ne ake yanka dabbobin domin sayarwa mabukata.

Wani bincike da hukumomi suka gudanar ya tabbatar da cewa jama’a na cin naman jakki a kasar ta Mali ne saboda araha, yayin da wasu ke amfani da shi saboda wasu dalilai masu nasaba da camfi.

Babbar matsalar da cin naman jakkin ke iya haifarwa kasar ta Mali da yankin Sahel dai ita ce karewar irin wannan na’uni na dabbobi da jama’a ke matukar amfani da shi saboda sauki wajen kiwo, da kuma taimakon sa wajen gudanar da sufuri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.