Isa ga babban shafi
Masar

An gano tarkacen jirgin saman EgyptAir a Tekun Bahrum

Jami’an Sojin sama da na ruwa a Masar sun sanar da gano buraguzen jirgin sama Fasinjan EgyptAir da ya yi hatsari a Tekun Baharrum dauke da mutane 66.

'Yan uwan Fasinjojin 'EgyptAir da ya yi hatsari a Meditterranian na cikin Zullumi
'Yan uwan Fasinjojin 'EgyptAir da ya yi hatsari a Meditterranian na cikin Zullumi KHALED DESOUKI / AFP
Talla

Sojojin sun sanar da tsinto kayayyaki Fasinjojin da wani sashe na jirgin a gabar ruwa dake da nisan Kilomita 290 daga arewacin Alexandria na Masar.

A safiyar yau juma'a aka fadada aikin neman jirgin saman, wanda ya bata tun a daren shekaranjiya laraba.A na kyautata zaton cewa jirgin wanda ya taso daga Paris a hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira ya bata ne a wani wuri da ke kan tekun Bahar Rum.

Sojojin sama da na ruwa tare da sauran kwararru daga kasashen Masar da kuma Girka sun fantsama kan tekun na Mediterranian bayan da aka bayar da labarin cewa an ga wani abu mai kama da buraguzen jirgin sama, to sai dai daga bisani an bayyana cewa buraguzen ba na wannan jirgi ba ne.

Hakazalika akwai kwararre daga Faransa da kuma na kamfanin Airbus wanda ya kera wannan jirgi da ke taimakawa a wannan bincike, yayin da hukumomin kasar ta Masar ke cewa ba su kawar da tsammanin cewa bacewar jirgin ba ta da nasaba da ayyukan ta’addanci ba.

Yanzu haka dai ‘yan uwan mutanen da ke cikin jirgin na a cikin damuwa, bayan share sama da sa’o’i 24 ba tare da an samu labarin abinda ya yi sanadiyyar bacewar wannan jirgin ba.

A watan okotoban bara, wani jirgin saman fasinjan kasar Rasha dauke da mutane 224, ya tarwatse a sararin samaniyar kasar ta Masar, kuma bincike ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda ne suka dana bam a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.