Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyar Congo

Congo zata gurfanar da Katumbi

Jamhuriyyar demokuradiyar Congo ta caji Madugun adawa Moise Katumbi da laifin cin amanar kasa bayan ya ayyana kudirin shi na tsayawa takarar shugabancin kasar, a yayin da kotun kundin tsarin mulki ta ce shugaba Joseph Kabila na iya ci gaba da shugabanci ba tare da an kada kuri’a ba.

Madugun adawa a Congo Moise Katumbi
Madugun adawa a Congo Moise Katumbi © REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Ana kuma zargin Katumbi laifin hayan wasu daga kasashen waje ciki har da wani dogari da ke tsaronsa da ya dauko daga Amurka.

Haka kuma Masu gabatar da kara sun caji Katumbi da laifin yin zagon kasa ga tsaron kasa, kuma yanzu haka an bayar da sammacin kama shi.

Laifin da ake zarginsa ya shafi zartar da hukuncin kisa amma yanzu za a iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan soke hukuncin kisa a Jamhuriyyar Congo.

Sai dai babu wani lokaci yanzu da aka tsayar da za a soma shari’ar ta Katumbi, idan har an tabbatar da laifin da ake tuhumar shi.

Wannan dai na zuwa ne bayan matsin lamba da shugaba Kabila ke fuskanta daga ciki da waje a kokarin da ya ke na jinkirta zaben kasar a bana bayan kawo karshen wa’adin shugabancinsa na shekaru 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.