Kasashen duniya zasu taimakawa Najeriya wajen yakar Boko Haram
Da kamala taron kasa da kasa a Abuja,Shugabanin kasashen dake makwabtaka da Najeriya kama daga Nijar,Kamaru,Chadi,Benin sun sanar da hada karfi domin kawo karshen kungiyar Boko Haram.Yayinda Kasashen Duniya suka sanar da kawo nasu taimako a kai.
Wallafawa ranar:
Francois Hollande wanda yake halartan taro na kasa- da-kasa gameda annobar Boko Haram, na magana da manema labarai bayan ya gana da Shugaban Najeria Muhammadu Buhari a birnin Abuja.
Faransa zata bada taimakon da ya dace wajen yakar kungiyar Boko Haram,hakka zalika Birtaniya da Amurka sun sanar da kawo nasu kokarin a kai.
Shugaba Hollande ya ce shakka babu anyi nasarar gaske wajen murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram ya zuwa wannan lokaci.
Taron da ake yi a Abuja na samun halarcin shugabannin kasashen Benin, Kamaru, Chadi, da Niger wadanda dakarunsu ke cikin dakarun hadin guiwa 8,500 da za’a girke su a Chadi don share guggubin ‘yan Boko Haram da suka rage.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu