Isa ga babban shafi
Rwanda

Magadan garin Rwanda sun gurfana a Faransa

Wasu tsoffin magadan gari biyu na Rwanda na gurfana a wannan Talata a gaban kotun kasar Faransa saboda zargin su da aikata laifukan yaki da kuma rawar da suka taka wajen kisan kiyashin da aka yi a shekara ta 1994.

Wasu daga cikin kawunan kwarangwal din mutanen da suka rasa rayukansu a rikicin Rwanda shekaru fiye da 20 da suka gabata da aka ajiye a gidan tarihi na Nyamata da ke kasar ta Rwanda
Wasu daga cikin kawunan kwarangwal din mutanen da suka rasa rayukansu a rikicin Rwanda shekaru fiye da 20 da suka gabata da aka ajiye a gidan tarihi na Nyamata da ke kasar ta Rwanda Wikimedia Commons/Fanny Schertzer
Talla

Shari'ar dai ita ce karo na biyu da kotun ke yi wa mutanen da suka tsere tare da buya a Faransa bayan an zarge su da hannu a kisan kiyashin. 

Ana ganin shariar  ta yau za ta nuna irin tsamin dangantaka tsakanin kasashen Faransa da Rwanda.

Toffin magadan garin da ke fuskanatar shari'ar sun hada da Octavien Ngenzi mai shekaru 58 da kuma Tito Barahira mai shekaru 64 kuma dukkanin su sun rike mukamin magajin gari ne a Kabarondo.

A shekara ta 2009 ne, wata kotu a Rwanda da ake kira Gacaca ta yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin rai da rai a bayan idonsu.

Akalla mutane  dubu 800 ne suka rasa rayukansu cikin kwanaki 100 a tarzomar, yayin da Rwanda ke zargin Faransa da hannu a kisan kare dangin wanda ya auku fiye da shekaru 20 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.