Isa ga babban shafi
Rwanda

Zabtarewar kasa ta kashe mutane a Rwanda

Akalla mutane 20 akasarin su kananan yara zabtarewar kasa ta kashe a kasar Rwanda bayan a tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Rwanda na yawan samun zabtarewar kasa da kuma ambaliya
Rwanda na yawan samun zabtarewar kasa da kuma ambaliya Reuters
Talla

Kakakin ma’aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Frederic Ntawukuriryayo ya ce, zabtarewar kasar ta binne gidaje da dama a yankin Gakenke.

Kasar Rwanda mai dauke da tsaunuka na yawan samun ambaliya da zabtarewar kasar.

A cikin wannan shekarar kawai mutane 67 suka mutu, yayin da gidaje sama da dubu 1 500 suka rushe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.