Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar na son yanke hukuncin kisa akan Ma’aikatan al Jazeera

Kotun Masar ta bukaci zartar da hukuncin kisa akan mutane shida da suka hada da ‘Yan jarida uku da ake tsare da su tare da tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi.

Masar na fama da hare haren yan tawaye tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Morsi
Masar na fama da hare haren yan tawaye tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Morsi AFP PHOTO / STR
Talla

Sai dai hukuncin da kotun ta bukata bai shafi Morsi ba, amma ana sa ran kotun ta yanke masa hukunci a ranar 18 ga watan Yuni bayan kotun koli ta yi nazari akan shari’ar.

Ana dai tuhumar mutanen guda shida da suka hada da ma’aikatan tashar Al Jazeera da kuma Mohammed Morsi da cin amanar kasa kan wasu bayanan sirri da suka kwarmatawa Qatar.

Tuni dai aka zartarwa Morsi da hukuncin daurin rai da rai kan alaka da Iran da kungiyar Hamas da Hezbollah, da kuma wani daurin shekaru 20 akan rikicin da aka yi kusa da fadar shugaban kasa a 2012 tsakanin masu adawa da mulkin shi da kuma magoya bayan shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.