Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2016

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin kasar na 2016 a yau Juma’a bayan tsaikun da aka samu na tsawon wata guda sakamakon kura-kuran da aka samu a ainihin bukatun kasafin kudin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari statehouse
Talla

Shugaba Buhari ya sanya hannu ne kan kasafin kudin a fadarsa a Abuja a gaban Mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo da Ministocinsa da Shugaba Majalisar Dattijai.

An dai shafe lokaci ana samun sabani tsakanin fadar shugaban kasa da Majalisar dokoki kan kasafin kudin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisar a watan Disemba.

Sai dai kuma Buhari ya sanya hannu ne kan kasafin na Naira Tiriliyon 6.06, sabanin Tiriliyon 6.07 da ya gabatar tun da farko a Majalisa.

A lokacin da ya ke jawabi bayan sanya hannu kan kasafin, Shugaba Buhari ya ce wannan mataki ne da zai inganta tattalin arzikin Najeriya.

Kasafin na Najeriya da ke dogaro da arzikin fetir, an tsara shi ne akan farashin mai dala 38 duk ganga sabanin farashin man a yanzu dala 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.