An sace ma'aikatan Red Cross 3 a Congo
Wasu mutane dauke da makamai sun sace ma’aikatan kungiyar agaji ta Red Cross guda 3 a Jamhuriyar Dimokraddiyar Congo, mai Magana da yawun kungiyar Elisabeth Cloutier tace an sace ma’aikatan ne a Rutshuru dake kudancin kasar inda suka je gudanar da aikin su.
Wallafawa ranar:
Kakakin sojin kasar Capt Guillame Ndjike yace sun gargadi kungiyar da ta daina tura ma’aikata kauyuka ba tare da samun rakiyar jami’an tsaro ba.
Wannan dai bashi bane karon farko da ake sace ma'aikatan kungiyar dake aikin agaji a kasashen Afrika, alkaluman kungiyar na cewa ma'aikatan kungiyar 60 ne suka rasa rayukansu a sassan Afrika a shekara guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu