Isa ga babban shafi
Afrika

'Yar Ghana ce sarauniyar kyau a Afrika

Wata 'yar Ghana mai suna Rebecca Asamoah ta lashe kyautar sarauniyar da ta fi kowacce kyau a nahiyar Afirka, a wani biki da aka yi a kasar Afrika ta kudu.

Rebecca Asamoah ta Ghana wadda ta lashe sarauniyar kyau a Afrika
Rebecca Asamoah ta Ghana wadda ta lashe sarauniyar kyau a Afrika guardian.ng
Talla

'Yar shekaru 24 Rebecca Asamoah, wadda likitar hakora ce, ta doke 'yan takara 11 daga cikin 40 da suka shiga gasar wajen samun nasara a bikin da aka gudanar a Johannesburg.

Michelo Malamabo ta kasar Zambia ta zo ta biyu, yayin da Jemimah Kandimiri ta zo ta uku a gasar.

Bikin wanda shi ne irin  sa na farko, ya saba da yadda ake gudanar da zaben Sarauniyar kyau, musamman irin kayan da 'yan takarar ke sanyawa da kuma tikar rawar da suke yi na wakar Selif Keita.

Neo Mashishi, mai shirya fina- finai daga Afirka ta kudu ya kirkiro gasar da zummar karfafa 'yan matan Afrika da kuma nuna arzikin da Allah ya wadata nahiyar da shi.

Mashishi ya ce, yadda aka gudanar da bikin ya saba da yadda ake zaben Sarauniyar kyau ta duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.