Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun kaddamar da babban farmaki a Sambisa

Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da wani babban farmaki a dajin Sambisa cikin Jihar Borno domin kakkabe sauran mayakan kungiyar Boko Haram da suka rage.

Dakarun Najeriya a Dajin Sambisa
Dakarun Najeriya a Dajin Sambisa naij.com
Talla

Kwamandan rundunar Sojin ta lafiya Dole Janar Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai a garin Maiduguri cewa dakarunsu sun fadada farautar ‘Yan Boko Haram cikin dajin Sambisa.

Sannan ya ce sojoji sun samu gagarumar nasara a 'yan kwanakin nan akan ‘Yan Boko Haram inda suka murkushe wasu hare haren kunar bakin wake a kusa da dajin Sambisa da wasu hare haren da aka yi shirin kai wa a kauyuka da dama cikin Jihar Borno.

Kwamandan yace sun murkushe hare hare a Mudallah Ilage cikin karamar hukumar Dikwa da wasu hare haren a kauyukan Kyare da Ginba da Boboshe da Garna da Ajiri da Jidda.

Bayan Sojoji sun gano wata cibiyar da ‘Yan Boko Haram ke hada Bom, Kwamandan yace sun kuma kwato manyan makamai da suka hada da bindigogi kirar AK47 da albarussai da dama tare da 'yantar da mutane da dama daga hannun ‘Yan ta’adda.

Sai dai akwai wasu daga cikin sojojin Najeriya da suka samu rauni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.