Isa ga babban shafi
Kenya

Barazana ga makomar giwaye a Afrika

Shugaban kasar kenya Uhuru Kenyatta a jiya juma’a, ya bukaci kasashen duniya da su kawo karshen cinikin hauren giwa da ake yi daga Afirka zuwa yankin Asiya, wanda hakan ke barazana ga makomar giwaye a duniya.

Hauren Giwaye da aka kama a kasar Kenya
Hauren Giwaye da aka kama a kasar Kenya Harambee Kenya
Talla

Uhuru Kenyatta wanda ke jawabi a wani taron shugabannin kasashe da kuma kungiyoyin kare gandun daji, ya ce " matukar dai muka rasa giwayen da muke da su a Afrika, to hakan na a matsayin rasa abinda muka gada ne.Yanzu haka dai akwai giwaye da yawansu ya kama daga 450.000 zuwa 5000 a nahiyar Afrika, to sai dai alkaluma na nuni da cewa a kowace shekara ana kashe sama da 30.000 daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.