Chadi ta tsawaita dokar ta-baci don fada da Boko Haram
Gwamnatibn Chadi ta tsawaita dokar ta-baci na tsawon watanni shida domin dakile hare haren kungiyar Boko haram musamman a yankin tabkin Chadi. A jiya Talata ne Majalisar kasar ta amince da gagarumin rinjaye da matakin tsawaita dokar da aka kafa tun a 9 ga watan Nuwamba.
Wallafawa ranar:
Ministan tsaro Ahmat Mahamat Bachir ya ce dokar za ta taimaka ga murkushe ayyukan Boko Haram a yankin Chadi.
Sannan Ministan ya ce za su inganta tsaro a ciki da wajen kasar zuwa sassan yankin tabkin Chadi.
‘Yan Boko Haram dai sun addabi Kauyukan da suka kewaye tabkin Chadi da hare hare. Sannan suna ratsowa cikin kauyukan domin shiga cikin kasar.
Rundunar hadin guiwa ta kasashen tabkin Chadi da aka kafa da ta kunshi dakaru daga Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru ta taimaka wajen murkushe‘Yan Boko Haram.
Sai dai har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga tsaron kasashen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu