Ba fada mu ke ba, Jayayya muke da Buhari- Ndume
Sanata Mohammed Ali Ndume shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Najeriya ya ce ba fada suke da shugaba Buhari ba illa jayayya ga wasu fannonin da suke da sabani tsakanin bangaren Majalisa da zartarwa.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin fararen hula sun kaddamar da zanga-zanga domin adawa da ‘Yan majalisun Najeriya da suke zargin suna zagon kasa ga samun nasarar aiwatar da kasafin kudin bana a Najeriya.
Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu yace ba za su iya fada da shugabansu ba amma suna iya jayayya da shi kan bukatun da suke ganin ya dace a gyara.
A jiya Talata Masu zanga-zangar sun toshe hanyar zuwa Majalisa a Abuja tare yin kira ga shugaban Majalisar Dattijai Dr Bukola Saraki ya yi murabus.
Ndume yace babu wata girman zanga-zanga da za ta sa wani Dan Majalisa ya yi murabus. A cewar shi Zanga-zangar ta sabawa tsarin mulki domin akwai tsarin kiranye da ake yi akan duk wani Dan Majalisa.
Masu zanga-zangar dai sun bukaci ‘Yan majalisar su gaggauta kammala aikin da ya rataya akansu a kasafin kudin kasar, domin ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari damar aiwatar da ayyukan ci gaban raya kasa da ta yi alkawali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu