Isa ga babban shafi
Lafiya

Kasashen Afrika za su magance Malaria

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, akwai kasashe 6 na Afrika da za su iya kawo karshen zazzabin cizon sauro ko kuma Malaria daga shekara ta 2020.

Kimanin mutane miliyan 214 suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro a bara kuma kusan dubu 450 daga cikin su sun rasa yaukansu
Kimanin mutane miliyan 214 suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro a bara kuma kusan dubu 450 daga cikin su sun rasa yaukansu Getty Images AsiaPac/Paula Bronstein
Talla

A bayanin da ta fitar dangane da zagayowar ranar yaki da wannan cuta a duniya, hukumar ta lafiya ta bayyana kasashen Algeria da Botswana da Cape Verde da Comoros da Afrika ta Kudu da kuma Swaziland a matsayin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen fada da wannan cuta, tare da hasashen kawo karshenta a shekara ta 2020.

Sauran kasashen duniya da ake sa ran za su kawo karshen cutar nan da shekara ta 2020 sun hada da China da Malaysia da Koriya ta Kudu da kuma wasu kasashe takwas da ke yankin Lantin Amurka.

Wata sanarwa da hukumar lafiyar ta fitar a farkon wannan watan ta ce, nahiyar turai da  yankin tsakiyar Asiya da kasashen yankin Caucasus duk sun kawo karshen cutar ta zazzabin cizon sauro a cikin shekara ta 2015.

Kimanin mutane miliyan 214 ne suka kamu da wannan cutar a bara, inda kusan dubu 450 daga cikin su suka rasa rayukansu kamar yadda WHO ta ce.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.