Isa ga babban shafi
equatorial guinea

Ana dakon sakamakon zaben Guinea

Ana dakon sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar jiya lahadi a kasar Equatorial Guinea, inda Teodoro Obiang Nguema, wanda ya fi kowane shugaba dadewa akan karagar mulkin nahiyar Afrika ke fatan sake samun wani wa’adi na mulkin kasar.

Ana sa ran bayyana sakamakon zaben Equatorila Guinea nan da ranar Alhamis mai zuwa
Ana sa ran bayyana sakamakon zaben Equatorila Guinea nan da ranar Alhamis mai zuwa STR / AFP
Talla

Nguema mai shekaru 73 a duniya, ya dare kan karagar mulki kimanin shekaru 36 da suka gabata, yayin da ya bayyana cewa zai samu fiye da kashi 90 cikin 100 na zaben a wannan karan.

Tuni dai ‘yan adawa suka ce, yin magudi a zabukan kasar ba sabon abu bane, abinda ya sa wasu daga cikinsu suka kaurace wa zaben na wannan karan.

Masu sa ido kan zaben sun ce, an samu karancin fitowar masu kada kuri’u a wasu yankunan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.