'Yan Adawa A Kasar Chadi Sun Kushe Sakamakon Zaben Kasar
‘Yan adawa a kasar Chadi sun soki sakamakon zaben kasar da akace Shugaba maici Idris Derby Itno ya lashe domin zarcewa da mulkin kasar wa'adi na biyar a jere.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka dai Fira Ministan Albert Pahimi Padacke ya roki jama'a dasu kwantar da hankulan su.
Bayan sanar da cewa Idris Derby Itno ne yayi nasarar cin zaben , masu goyon bayan shugaban sunyi da nuna farin cikin su tare da harba bindigogi sama suna zagaya birnin N’Djamain.
Sakamakon zaben na nuna Shugaba mai ci Idris Derby Itno ya sami kuri'u kashi kusan 62%, yayin da Saleh Kebzabo na 'yan adawa ke da yawan kuri'u kusan kashi 13%.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu