Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Biafra sun musanta kisan Fulani

Kungiyar da ke hankoron kafa kasar Biafra a Najeriya ta musanta zargin tana da hannu wajen kisan Fulani ‘yan arewacin kasar da ke zama yankinsu. Emma Nmezu kakakin kungiyar  da ya musanta zargin cewa suna kisan Fulani ya shaidawa RFI cewa Fulani ne ke kashe mutanensu.

Shugaban masu da'awar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, na fuskantar tuhumar cin amanar kasa a Najeriya
Shugaban masu da'awar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, na fuskantar tuhumar cin amanar kasa a Najeriya AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Sannan ya zargi gwamnatin Buhari da kashe ‘Yan Biafra.

A karshen makon jiya ne dai Jami’an hukumar ‘Yan sanda ta fairn kaya DSS suka ce sun gano wani makeke kabari shake da gawarwakin Fulani da ‘Yan Biafra suka kashe a Jihar Abia.

DSS tace ta gano kabarin ne a dajin Umuanyi kusa da garin Aba inda aka binne Fulani sama da 50.

Akwai wasu Fulani 5 da aka kashe a makon jiya kamar yadda Wasu shugabanninsu a yankin kabilar Ibo suka tabbatar wa RFI Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.