Ana Zabe Na Shugaban Kasa a Chadi
Alummar kasar Chadi na gudanar da babban zaben kasar yau lahadi, inda ‘yan takara 12 ke fafatawa da shugaba mai ci Idris Derby Itno wanda ya kwashe shekaru 26 yana mulkin kasar.
Wallafawa ranar:
Shi dai Idris Derby na neman wa'adi na biyar ne domin mulkin kasar.
Dan shekaru 63, a zamanin mulkin sa ne kasar ta sami man fetur, kuma yanzu haka ta shiga kasashen duniya wajen yakar masu ikirarin jihadi.
Kan gaba cikin masu ja da shugaban akwai Saleh Kebzabo, musulmi daga yankin dake da yawan mutane na kudu maso yammacin Mayo Kebbi, wanda ya taba ja da shugaba Idris Derby a zaben shekara ta 1996
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu