Shugaba Ismail Omar Guelle na Djibouti ya Sake Lashe Zaben Kasar
Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh , wanda yake shugabancin kasar tun shekara ta 1999 ya sake lashe zaben kasar da aka gudanar Juma’a, karo na hudu a jere.
Wallafawa ranar:
Hukumomin kasar sun bayyana cewa Shugaban kasar ya sami yawan kuriu kashi 86.68% na yawan kuriu da aka jefa.
A jawabin sa Shugaban kasar mai shekaru 68 ya godewa al'ummar kasar saboda sake zaben sa da akayi.
A shekara ta 2011 Fira Ministan kasar ya sanar da nasarar shugaban kasar ta su a zaben kasar tun kafin a kammala tattara kuri'u, amma kuma tunda akace shugaban kasar mai shekaru ya sami yawan kuri'u fiye da kashi 50% sai aka sanar da cewa ya lashe.
Mutane dubu 187 ne suka chanchanci jefa kuria a zaben daya gabata a fadin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu