Isa ga babban shafi
Nijar

Kotun tsarin mulki a Nijar, ta tabbatar da sahihancin zaben

Kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar, ta tabbatar da sahihancin zaben da aka yiwa Issoufou Mahamadou a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka yi a ranar 20 ga wannan watan maris.Kotun tsarin mulkin ta ce Issoufou Mahamadou ya samu kashi 92, 51 cikin dari yayin da abokin hamayyarsa Hama Amadou ya samu kashi 7,49 cikin dari a zaben. 

Yan siyasar Jamhuriyar Nijar
Yan siyasar Jamhuriyar Nijar
Talla

‘Yan adawa a Nijar sun bukaci a saki dukkanin fursunonin siyasa kafin shiga tattaunawa da gwamnatin kasar.
Har ila yau wani lokaci a can baya ‘yan adawar sun bukaci a kafa gwamnatin rikon kwarya wadda za ta shirya sabbin zabubuka a kasar, to sai dai a cewar Zakary Oumarou, memba a jam’iyyar PNDS tarayya, wasu daga cikin bukatun ‘yan adawar sun kaucewa doka.
A jibi asabar ne za a rantsar Issoufou akan wa’adin mulkin kasar na shekaru biyar masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.