Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan adawar Nijar sun yi na’am da tayin tattaunawa

‘Yan adawan Jamhuriyar Nijar sun sanar da matsayin su cewar a shirye suke su tattauna da shugaban kasar Mahamadou Issofou bayan kauracewa zaben kasar da suka yi da aka gudanar a ranar 20 ga watan Maris zagaye na biyu.

Shugaban kasar Niger Mahamadou Issoufou da Hama Amadou babban mai adawa da shi.
Shugaban kasar Niger Mahamadou Issoufou da Hama Amadou babban mai adawa da shi. AFP/Issouf Sanogo/Farouk Batiche/Montage RFI
Talla

‘Yan adawar sun amince a zauna a tattauna a wata ganawa da aka yi jiya Litinin tsakanin wakilansu da Firaminsita Braji Rafini,

Dayyabu Abdusalam daga wakilan COPA ya shaidawa RFI cewa sun yarda a zo a tattauna bayan sun gabatar da korafe korafensu ga gwamnati da suka hada da matsalar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Sannan ya ce sun karbi sakon shugaban kasa daga Firaminista na neman hadin kai domin tunkarar matsalolin Nijar da suka hada da kalubalaen tsaro da hada kan ‘yan kasa don ci gaba.

Yanzu dai ya rage ‘Yan adawar su tabbatar da bayar da hadin kansu ga shugaba Issoufou wanda ya lashe zaben da aka gudanar zagaye na biyu da sama da kashi 92 tsakanin shi da abokin takararsa Hama Amadou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.