Isa ga babban shafi
Congo-Rwanda

Congo ta mikawa Rwanda Ntaganzwa domin hukunta shi

Gwamnatin Jamhuriyar demokradiyar Congo ta mikawa hukumomin Rwanda wani tsohon Magajin Gari da ake zargin yana da hannu wajen kisan kiyashin da akayi na mutane sama da 800,000 a shekarar 1994.

Ladislas Ntaganzwa
Ladislas Ntaganzwa Stephanie AGLIETTI / AFP
Talla

An kama Ladislas Ntaganzwa ne a watan Disamba a Gabashin kasar Congo sakamakon neman sa ruwa ajallo da akeyi saboda samun sa da laifin tinzira jama’a da kuma aikatan kisan kai da fyade a Yankin Nyakizu dake kasar ta Rwanda.

Kasar Amurka tayi tayin bada ladar Dala miliyan 5 ga duk wanda ya tsegunta inda za’a same shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.