Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bukaci bankuna dasu taimakawa bangaren noma

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatin kasar na hana shigowa da abinci daga kasashen waje, sai dai yace akwai shirin tallafawa manoma wajen ganin sun noma abincin da ake bukata a kasar.

Kasuwar manoma doya a Najeriya
Kasuwar manoma doya a Najeriya thenationonlineng.net
Talla

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne wajen bude taron Majalisar Tattalin arzikin kasa inda yake cewa abin takaici ne yadda manoma ke tafka asarar kayan marmari da suke nomawa wadanda ke bukatar masana’antu su sarrafa su.

Shugaban ya de bukaci bankunan ‘yan kasuwa dasu rage kudin ruwan da suke dorawa manoman inda ya baiwa babban bankin kasar umurnin sanya hannu wajen baiwa manoman rance.

Ana dai fama da tsadar abinci a kasar a yayin da Manoma a Najeriyar ke ci gaba da kokawa da rashin kayayyakin inganta noma kamar su taki da magungunan kashe kwari baya ga rashin tallafi daga gwamnati wajen bunkasa harkokin noma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.