Isa ga babban shafi
Nijar

Har yanzu ba a kai Hama Amadou a asibiti ba

Magoyan bayan Hama Amadou wanda zai kara da shugaban kasar mai ci Issoufou Mahamadou, sun ce har yanzu suna jira a bai dan takararsu a zabe mai zuwa damar ganin likitansa, bayan da a jiya juma’a ministan shari’ar kasar ya sanya hannu kan kuduri doka da ke bayar da yin hakan.

A hagu, Hama Amadou sai Mahamadou Issoufo a hannun dama
A hagu, Hama Amadou sai Mahamadou Issoufo a hannun dama AFP/Issouf Sanogo/Farouk Batiche/Montage RFI
Talla

Bayanan farko dai sun ce Hama Amadou ya isa a wani asibiti da ke Yamai, amma daga bisani aka tabbatar da cewa har yanzu yana Filingue inda ake tsare da shi, kuma dalilan da ake bayarwa su ne jirgin saman da ya kamata ya dauko shi ba ya cikin koshin lafiya.

A daya bangare kuwa gamayyar kungiyoyin ma’aikatan kwadago a Jamhuriyar Nijar sun bukaci a shiga tattaunawa ta kai-tsaye tsakanin gwamnati da ‘yan adawa, domin ganin cewa an gudanar da tsaftaccen zabe a ranar 20 ga wannan wata a kasar.

ITN, wadda ta kunshi manyan kungiyoyin kwadagon kasar guda 7, a sanarwar da ta fitar a birnin Yamai a wannan asabar, ta yi kakkausar suka a game da yadda bangarori biyu na siyasar kasar ke furta kalamai wadanda za su iya kawo mummunar baraka a tsakanin al’ummar kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.