Isa ga babban shafi
Najeriya

Switzerland za ta dawo wa Najeriya da wasu kudaden Abacha

Kasar Switzerland ta amince ta dawo wa Najeriya da kudi dala miliyan 321 daga cikin kudaden da Tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya sace. Kasashen biyu sun amince da yarjejeniyar dawo da kudaden ne a yau Talata.

Tsohon Shugaban Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha
Tsohon Shugaban Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha AFP
Talla

Hukumomin kasashen biyu sun sanar da cim ma yarjejeniyar ne bayan wata ganawa tsakanin Mataimakin shugaban Najeriya da hukumomin kasar Switzerland a birnin Tarayya Abuja.

Sannan kasashen biyu sun amince da yarjejeniyar dawo da wasu kudaden da jami’an gwamnati suka sace zuwa Switzerland.

Ana zargin tsohon Shugaban Najeriya marigayi Janar Sani Abacha da sace kudade da suka kai dala biliyan 2.2 a zamanin shugabancin shi tsakanin 1993 zuwa rasuwar sa a 1998.

Switzerland ta ce ta dawo wa da Najeriya da dala miliyan 720 daga cikin kudaden Abacha a shekaru 10 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.