Isa ga babban shafi
Ghana

Mutane 53 sun mutu a hadarin mota a Ghana

Yan sanda a kasar Ghana sun tabbatar da mutuwar mutane 53 sakamakon wani mummunan hadarin mota daya rutsa dasu, bayan da wata motar makare da Tumatiri tayi taho mu gama da wata babbar motar fasinja, abunda yayi sanadin mutuwarsu nan take.

Tutar kasar Ghana
Tutar kasar Ghana
Talla

Akwai kuma wasu mutane 23 da suka jikata a hadarin da yanzu haka ake kulawa dasu a asibiti, Wannan dai shine mummunan hadarin motar da kasar ta fuskanta cikin wannan shekara.

Tuni dai shugaban kasar John Mahama ya aika da sakon ta’azziya ga iyalan mamatan inda ya bayyana hadarin a matsayin abin bakin ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.