Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

An soma zabe a Afrika ta Tsakiya

A yau lahadi ne yan kasar Afrika ta Tsakiya ke gudanar da zaben shugaban kasa da na yan Majalisu.Akala mutane millyan biyu ne hukumar zaben kasar ta sanar da cewa sun samu yi rijista. 

Zaben kasar Afrika ta Tsakiya na yau lahadi
Zaben kasar Afrika ta Tsakiya na yau lahadi REUTERS/Media Coulibaly TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Zaben na yau zai hada yan takara Anicet Georges Dologuele da Faustin Archange Touadera.
Zaben wata hanyar da zata kawo karshen yakin da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya tun bayan kawar da tsofuwar Gwamnatin shugaba Francois Bozize a shekara ta 2012.
Haka zalika Michel Djotodia yayi kasa a guiwa bayan kawar da shi ,uwargida Catherine Samba Panza ta karbi shugabanci Gwamnatin wucin gadi a watan janairu shekarar 2014.
Rahotani daga babban birnin kasar Bangui na nuni cewa mutane sun soma isa ruhunan zabe domin gudanar da zabin su.

Hukumomi a  kasar sun sanar da daukar tsauraren matakan tsaro  domin gujewa duk wani tashin hankali kamar dai yadda aka gani a zaben baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.