Isa ga babban shafi
WHO-Zika

Zika barazana ce ga Afrika

Masana lafiya sun yi gargadi akan yiyuwar bullar cutar Zika a kasashen Afrika saboda nasabarsu da kasashen da ke fama da cutar yanzu haka a latin Amurka.

Masana kiyon lafiya sun yi gargadi akan Zika a Afrika
Masana kiyon lafiya sun yi gargadi akan Zika a Afrika REUTERS/Jorge Cabrera
Talla

Masanan sun bukaci a gaggauta daukar matakan kariya domin dakile bullar cutar a Afrika bayan gano wasu na’uin Sauro da ke dauke da Zika.

Cutar Zika na ci gaba da bazawa zuwa sassan duniya bayan ta zama annoba a kasashen Latin da Caribbean, masana masu binciken lafiya suna ganin Cutar na dab da rarrfowa zuwa tushenta Nahiyar Afrika.

A wani dajin Uganda ne na Entebbe aka fara samun cutar Zika a 1947. Yanzu haka kuma hukumar lafiya ta duniya ta kaddamar da dokar ta-baci domin yakar cutar bayan ta bulla a kasashe 27 yawancinsu a kasashen Latin Amurka har zuwa Caribbean zuwa Amurka da China da Australia.

Sai dai masana na ganin alakar wasu Afrika da kasashen da suka yi masu mulkin mallaka na tasiri ga shigowar cutar cikin lokaci kankani musamman kasar Cape Verde da rahotanni suka an samu Mata masu juna biyu da dama da suka kamu da Cutar ta Zika.

Portugal ce ta yi wa Cape Verde mulkin mallaka kuma alakar harshen Fotuganci tsakanin kasar da kasashen Latin da ma fi yanwaci ke magana da harshen na iya zama barazana ga Afrika.

kwararrun masana binciken lafiya sun bukaci kasashen Afrrika su tashi tsaye domin daukar matakan rigakafin cutar kafin ta yadu.

Afrika dai na cikin yankunan duniya da ke fama da sauro kuma masu bincike sun ce sun gano na’uin sauro kusan 20 da ke dauke da Zika a Afrika.

Sai babu tabbaci ko Sauron Afrika suna a iya yada cutar ga mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.