Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutane a Kamaru

Akalla mutane 6 sun rasa rayukansu yayin da kimanin 50 suka jikkata sakamakon tagwayen hare haren bama bamai da aka kaddamar a arewacin Kamaru a wannan laraba.

Boko Haram ta sha kai famaki a arewacin Kamaru
Boko Haram ta sha kai famaki a arewacin Kamaru Youtube
Talla

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, ‘wasu 'yan mata guda biyu ne suka kashe mutanen a harin kunar bakin waken bayan sun tarwatsa kansu da bama baman da su ke dauke da su a kauyen Nguetchewe da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya.

Majiyar ‘yan sanda ta ce, kananan yara da dama na cikin wadanda lamarin ya ritsa da su.

Kungiyar Boko Haram dai ta sha kai farmaki tare da hallaka mutane a yakin arewacin Kamaru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.