Isa ga babban shafi
Bangui

Faransa za ta binciki zargin lalata a Afrika ta tsakiya

Masu bincike daga Faransa za su bincike zargin cin lalata da kanana yara da ake yi wa sojojin kasar da aikatawa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Zargin ya biyo bayan Rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ta bankaado sabbin zarge-zarge Lalata da yara da dakarun wanzar da zaman lafiya suka aikata a Afrika ta tsakiya.

Dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya
Dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Rahoton dai ya Ambato Yaran na bayyana yadda sojojin ke lalata da su ta hanyar ba su abinci da biskit a matsayin tukuici, kuma wannan ba shi ne karo na farko da ake zargin sojojin Faransa daaikata wannan laifi ba.

Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya dai na kokarin farfadowa ne daga rikicin siyasar kasar tun bayan juyin mulkin shekarar 2011 wanda ya rikide ya koma rikicin addini da Kabilanci.

A makon jiya gwamnatin Congo tace tana binciken zargin da ake yi wa dakarunta cikin rundunar Afrika ta MINUSCA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma zargi dakarun EUFOR na Tarayyar Turai da aikata lalatar.

Batun lalata da kananan yara na cigaba da zama ruwan dare tsakanin dakarun da ake aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya, duk da korar shugaban Rundunar Sojin da Ban ki-moon ya yi a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.