Congo na bincike kan yi wa mata fyade a Afrika ta tsakiya
Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta ce, ta kaddamar da bincike game da zarge-zargen da ake yi wa dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya na cin zarafin kananan yara mata ta hanyar yi musu fyade.
Wallafawa ranar:
Ministan yada labarai na Congo, Thierry Moungalla ya bayyana cewa, sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna da ofishin sakatare janar na majalisar dinkin diniya kan cewa za su gudanar da bincike kan lamarin.
Binciken wanda ma’aikatar tsaron kasar za jaogaranta, zai yi kokarin gano ainihin girman zarge-zargen da ake yi wa dakarun da suka hada da na Jamhuriyar Congo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu