Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zimbabwe na fama da matsanancin fari

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya ayyana kasar a matsayin mai hadari sakamakon fari da ya ce ya shafi kauyukan kasar da dama, inda kusan rabin mutanen kasar ke fama da matsanancin rashin abinci. 

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Shugaba Mugabe ya danganta matsanancin karancin abincin ne da rashin kyawun damina saboda sauyin yanayi, ga kuma munanan takunkuman da kasashen Turai suka kakaba wa kasar.

Kasar Zimbabwe wadda a baya ake yi mata kirari da cewa tana iya ciyar da kasashen Afrika, na fama da matsalolin a ‘yan shekarun nan, al'amarin da ala tilas ya sa ta dogaro da kasashen waje don samun tallafi.

Ministan ayyukan musamman na jama'a Saviour Kasukuwere, ya fadi cikin wata sanarwa cewa mutane miliyan daya da dubu dari biyar na cikin mawuyacin hali, yayinda yankunan karkaru 60% an gaza cin amfanin gona.

A cewar ministan, shanu  dubu 16 da 500 suka mutu saboda rashin abinci.

Masu adawa da shugaba Robert Mugabe na ganin cewa an shiga wannan mawuyacin halin ne saboda matakan da shugaba Mugabe ya bullo da su na kwace filaye daga turawa a shekara ta 2000.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.