Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

An ceto mahaka ma'adinai 87 daga karkashin kasa a Afrika ta kudu

A kasar Afrika ta kudu, sama da mahaka zinari 80 aka yi nasarar cetowa a yau jumma’a bayan sun makale a karkashin kasa a wani kamfanin hakar ma’adinai mallakin kasar Asutralia yayin da har yanzu ake ci gaba da neman mutane uku daga cikin su.

Wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinan karkashin kasa na Goldfields
Wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinan karkashin kasa na Goldfields REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A cikin wata sanawar da ya fitar, kamfanin hakar zinararin mai suna Vantage Goldfield ya bayyana cewa ma’aikatansa 87 ne suka makale a karkashin kasar amma anyi nasarar ceto su.

Al-amarin dai ya faru ne a bakin babbar kofar shiga cikin kamfanin yayin da rahotanni suka tabbatar cewa, babu wanda ya mutu daga cikin mahakan.

A farko dai shugaban kamfanin, Mike McChesney da kuma kungiyar ma’aikatan hakar ma’adinan karkashin kasa na Afrika ta kudu sun fadi cewa, mutane 115 ne hadarin ya cika da su yayin da daga bisa kungiyar ta sake cewa mutane 78 ne suka makale a karkashin kasar.

Har yanzu dai ba a gano dalilin da ya haifar da rubtawar kasar ba kamar yadda mai mgana da yawun kungiyar mahakan Manzini Zungu ya sanar.

A bara dai kimanin mahakar ma’adinai 77 ne suka rasa rayukkansu a irin wannan hatsarin yayin da a shekarar 2014 mutane 84 suma suka  gamu da ajalinsu a irin hatdarin.

Kamfanin dai na Vantage Goldfields na da reshe a garin Barberton da ke lardin Mpumalanga na Afrika ta kudu.

Wuraren hakar ma’adinan karakshin kasa na Afrika ta kudu su suka fi zurfi da hatsari a duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.